Ta'addanci

Ta'addanci ba koyarwar Annabi ba ne-Qaribulla Kabara

Jagoran Darikar Qadiriya a Afrika, Dr. Qaribullah Nasir Kabara.
Jagoran Darikar Qadiriya a Afrika, Dr. Qaribullah Nasir Kabara. RFI/Hausa/Abdoulkarim

A yayin da tashe-tashen hankulan da ake dangantawa da addinin Islama ke ci gaba da karuwa a wasu kasashen duniya, Shugaban Darikar Qadiriyya na Afrika Dr. Qaribullah Sheikh Nasir Kabara ya bayyana cewa, Annabi Muhammad Mai Tsira da Aminci bai koyar da ayyukan ta’addanci ba face zaman lafiya da mu’amalar arziki da sauran mabiya addinai mabanbanta.

Talla

A yayin zantawa da sashen Hausa na Radio France International a birnin Lagos na Najeriya, Dr. Qaribullah ya bayyana yadda Sufaye suka yada addinin Musulunci cikin lumana ba tare da zubar da jini ba musamman a kasashen Afrika.

A cewar Shehun Malamin, Mazan Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi kyakkyawar zamantakewa da Yahudawa a birnin Madina a zamaninsa, yayin da Sarkin Habasha ya sauya addininsa daga Kirista zuwa Musulunci saboda yadda Annabi ya yi zaman lafiya da su.

Malamin ya kara da cewa, kasashen duniya da aka kafa su kan tsarin Sufanci na kan gaba wajen samun zaman lafiya a duniya, inda ya bayar da misali da kasar Morocco.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da muka yi da Dr. Qaribullah Nasir Kabara.

Muryar Dr. Qaribullah Nasir Kabara

Wannan na zuwa ne a yayin da wasu kungiyoyin ta’addanci a sassan duniya ke yada akidar kashe-kashe da tsangwama, inda suke danganta hakan da koyar addinin Islama.

Baya ga Dr. Qaribullah, Malaman Islama da dama sun jaddada cewa, babu inda addinin Musuluci ya umarci kaddamar da hare-hare kan sauran mabiya addinai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.