Duniya

Jawabin shugaban Rasha ya haifar da muhawara

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin Sputnik/Aleksey Nikolskyi/Kremlin/Reuters

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya gabatarwa da majalisar kasar kudurin neman yin zaben raba gardama kan yiwa wasu sassan kundin tsarin mulki kwaskwarima, domin karfafa ayyukan ‘yan majalisar.Putin ya gabatar da wannan kuduri ne, yayin jawabi kan lamurran kasa a yau, da ya saba gabatarwa a zauren majalisar kasar duk shekara.

Talla

A lokacin da yake gabatar da jawabin sa Putin bai ce komai kan makomar shugabancinsa idan wa’adinsa na 4 ya kare a shekarar 2024 ba, jawabin shugaban ya haifar da hasashe da kuma muhawara a ciki da wajen Rasha kan makomar siyasarsa bayan shafe sama da shekaru 20 yana jagorantar kasar.

Sama da manyan kusoshin gwamnatin Rasha dubu 1 da 300 ne suka halarci taron jawabin na shugaba Putin, wanda ya zo yayinda kasar ke shirin gudanar da zaben ‘yan majalisa a shekarar 2021, a dai dai lokacin da jam’iyya mai mulki ta United Russia ke fuskantar koma bayan karbuwa da take da shi tsakanin al’ummar kasar.

A shekarar 1999 Vladmir Putin dare kan shugabancin Rasha bayan murabus din bazatar da shugaba a waccan lokacin Boris Yeltsin yayi, tun daga lokacin ne kuma ya ci gaba da rike madafun ikon kasar, ciki har da rike mukamin Fira Ministan kasar, lokacin da babban amininsa Dmitry Medvedev ya karbi kujerar shugabancin kasar a shekarar 2008 na tsawon shekaru 4.

Firaministan Rasha Dmitri Medvedev da majalisar ministocinsa sun yi marabus jim kadan bayan jawabin da shugaba Vladimir Putin ya gabatar a yau laraba.

Medvedev, ya ce sun dauki matakin yin marabus ne domin bai wa shugaban damar aiwatar da sauye-sauyen da yake bukata ciki har da yi wa kundin tsarin mulki gyara.

Bayan sake zabar shugaba Putin a matsayin shugaban Rasha a wa’adi na 4 a 2018, wata kuri’ar jin ra’ayi ta nuna cewar farin jininsa ya ragu zuwa matakin kashi 70 a tsakanin ‘yan kasar, idan aka kwatanta da zangon mulkinsa na 3, lokacin da karbuwarsa ta kai kashi 80 cikin 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.