Isa ga babban shafi
Iran

Makamai masu linzami ne suka kakkabo jirgin Ukraine

Jami'an tsaro na bincike a wurin da hatsarin jirgin Ukraine ya auku a birnin Tehran
Jami'an tsaro na bincike a wurin da hatsarin jirgin Ukraine ya auku a birnin Tehran © Nazanin Tabatabaee/WANA (West Asia News Agency) via REUTERS
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 Minti

Wani sabon bidiyo ya nuna yadda makamai biyu masu linzami suka kakkabo jirgin saman Ukraine a birnin Tehran na Iran, inda daukacin fasinjoji 176 suka rasa rayukansu.

Talla

Jaridar New York Times ta ce, ta tabbatar da sahihancin kyamarar tsaron da ta dauki wannan bidiyon amma babu daya daga cikin makaman biyu da ya yi nasarar kakkabo jirgin kasa nan take.

Bidiyon ya nuna jirgin na Ukraine na shawagi na tsawon mintina da dama a sararin samaniya duk da cewa, yana ci da wuta kafin daga bisani ya yi hatsari bayan ya rikito kasa.

Jaridar ta ce, makamin farko ya jikkata na’urar sadarwar jirgin kafin a harba masa makami na biyu.

An dauki tsawon kwanaki mahukuntan birnin Tehran na ci gaba da musanta rahotannin da ke cewa, an kakkabo jirgin ne samfurin Boeing 737-800.

Sai dai daga bisani rundunar saman sojin juyin juya halin Iran ta amsa cewa, ita ce ta harbo jirgin da makamai mai linzami cikin kuskure.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, aka wallafa bidiyon farko da ke nuna yadda aka yi amfani da makami mai linzami wajen harbo jirgin saman na Ukraine.

Wannan na zuwa ne bayan harin saman da Amurka ta kaddamar a Iraqi, inda ta kashe kwamandan sojin Iran Qassem Soleimani, lamarin da ya tsananta tankiya tsakanin Washington da Tehran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.