Amurka

Zaman Majalisa dangane da batun tsige Donald Trump nan gaba

shugaban Amurka Donald Trump.
shugaban Amurka Donald Trump. Reuters

Akwai yiyuwar majalisar dattawan Amurka ta fara zama don tafka mahawarar kan batun tsige shugaba Donald Trump a ranar talata mai zuwa, kamar yadda shugaban masu rinjaye a majalisar Mitch McConnell ya sanar a yau Laraba.

Talla

Majalisar dattawan wadda magoya bayan jam’iyyar Republican ke da rinjaye a cikinta, na shirin fara mahawarar kan wannan batu ne bayan majalisar wakilai inda Democrat ke da rinjaye ta amince da matakin tsige shugaba Trump.

Wannan matakin dai shi ne na karshe da zai tilastawa shugaba Trump gurfana gaban ‘yan majalisar dattijai, domin fuskantar tuhume-tuhumen da ake masa na gayyatar Ukraine ta yi katsalandan a zabukan Amurka, da kuma amfani da karfin ikonsa ta hanyar da bata dace ba.

Wannan mataki da aka shiga, ya sanya Donald Trump zama shugaban Amurka na 3 a tarihi da zai gurfana gaban ‘yan majalisun kasar, bisa tuhumarsa da aikata laifukan da za su kai ga tsige shi daga karagar mulki.

Sai dai wasu magoya bayan shugaban harma da shi kansa, na ganin zai yi wahala kudurin tsige shin ya samu shiga a zauren majalisar dattijan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.