Australia

Ruwan sama ya fara kashe gobarar dajin Australia

Wutar dajin Australia.
Wutar dajin Australia. PETER PARKS / AFP

Saukar ruwan sama a wasu sassa na yankin gabashin Australia ya kawo sassauci ga ibtila’in gobarar dajin da kasar ke fuskanta fiye da watanni biyu, gobarar da masana suka alakanta da guda cikin illolin dumamar yanayi ga duniya.

Talla

Da safiyar yau Alhamis ne al’ummar Australia suka wayi gari da mamakon ruwan saman wanda ya yi karfi a dazukan da ke fama da gobarar, dai dai lokacin da masu hasashen yanayi ke ganin kasar na iya ci gaba da fuskantar mamakon ruwa a ‘yan makwannin nan.

Saukar ruwan tare da hasashen masanan ya sanyaya zukatan al’ummar yankin na gabashin Australia musamman ga dazukan kudancin Wales yankin da wutar dajin ta fi banna fiye da ko’ina, inda suke fatan ruwan ya yi sanadin kawo karshen gobarar da kuma sanyaya gari daga tsananin zafin da ake fuskanta yanzu haka.

Wutar dajin ta Austrlia da ke ci gaba da banna fiye da watanni biyu, masu fafutukar yaki da dumamar yanayi sun yi imanin ta na da nasaba da hakar makamashin Coal da gwamnatin kasar ke ci gaba da yi, wanda ke gurbata yanayi baya ga haddasa gobarar wadda kawo yanzu ta hallaka mutane 28 baya ga miliyoyin dabbobin da ke rayuwa a cikin dazuka.

Kafin yanzu dai, yankunan da ke fama da ibtila’in gobarar dajin na fuskantar tsananin zafi yayinda ruwan sama ya dauke dungurugum dai dai lokacin da ake ci gaba da kai ruwa rana a kokarin kashe gobarar.

Cikin sakon hukumar kashe gobarar ta Wales a yau Alhamis, ta bayyana cewa saukar ruwan ya saukakawa hatta jami’anta gudanar da aiki, bayanda kusan rabin gobarar da ake fuskanta a dazukan kasar 30 suka fara lafawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.