Amurka

Amurkawa sun soki kudirin takaita mallakar bindiga

Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da dokar takaita mallakar bindiga a Amurka.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar adawa da dokar takaita mallakar bindiga a Amurka. REUTERS/Michael A. McCoy

Dubban masu ra'ayin mallakar bindiga a Amurka sun yi dandazo a wani katafaren dandali a babban birnin jihar Virginia na kasar don kalubalantar kudirin da ke neman takaita mallakar bindugu a jihar, gangamin da ya gudana bisa tsauraran matakan tsaro baya ga dokar ta bacin da hukumomi suka ayyana.

Talla

Masu gangamin cikin shigar mafarauta sun hallara a dandalin Capitol bayan cajesu don gudun kar su shiga da makamai, yayinda wasu da suka ki amincewa da matakin cajesu suka tsaitsaya a waje rike da bindigogi.

Wasu bayanai sun ce dandazon masu ra'ayin mallakar bindigar sun rika daga tutar jihar Virginia baya ga wani kyalle da ke dauke da hoton sharbebiyar bindiga da kuma wani rubutu da ke cewa ''Muga wanda zai hana mu mallakar bindiga'' yayinda wasu kuma suke daga kyallen da ke rubuce da cewa '' Sai ku karbe mu gani''

Gangamin wanda wata kungiyar 'yan asalin jihar ta Virginia ta shirya, na da nufin kalubalantar kudirin dokar takaita mallakar bindiga a jihar da Jam’iyyar Democrats mai jagorancin jihar ta gabatar.

Kungiyar ta caccaaki abin da ta kira yin karan tsaye ga dokar Amurkan da ta sahalewa al'umma damar mallakar makamai, dokar da ke ci gaba da haddasa cecekuce a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.