Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisar Amurka na ci gaba da zaman jin bahasin tsige Trump

Majalisar Amurka yayin zaman sauraron bahasin tsige Trump.
Majalisar Amurka yayin zaman sauraron bahasin tsige Trump. REUTERS/U.S. Senate TV/Handout via Reuters
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu | Bashir Ibrahim Idris
Minti 2

'Yan Jam’iyyar Demokrat a Amurka sun fara gabatar da ba’asi a zauren Majalisar Dattawa da zummar ganin an tsige shugaba Donald Trump wanda su ke zargi da aikata laifi wajen tirsasawa shugaban Ukraine gudanar da bincike kan tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman ganin Jam’iyyar Dimokrat ta tsayar da shi takara, Joe Biden.

Talla

Shugaban kwamitin binciken Majalisar wakilai Adam Schiff, wanda ke jagorancin tawagar dake tuhumar shugaba Trump ya yiwa zaman Majalisar bayanai kan abinda ya kira kura kuran da shugaba Trump ya aikata wadanda suka sabawa dokokin Amurka.

Schiff yace da aka bankado laifin da Trump yayi, sai kuma yayi amfani da ofishin sa wajen katsalandan domin hana binciken sa.

Shugaban kwamitin ya bukaci Yan Majalisun Dattawa 100 dake kasar da su kauda banbancin jam’iyyar da suke da shi wajen yanke hukunci kan laifin da trump yayi domin nunawa Amurkawa cewar babu wanda yafi karfin doka a kasar.

Yanzu haka Jam’iyyar Trump ta Republican ke da Yan Majalisu 57 a Majalisar Dattawa, yayin da Dimokrat ke da 47.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.