Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisar dattijai ta soma muhawara kan batun tsige Trump

shugaban Amurka Donald Trump.
shugaban Amurka Donald Trump. SAUL LOEB / AFP
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

A jiya talata majalisar dattawan Amurka ta fara zama don tafka mahawarar kan batun tsige shugaba Donald Trump kamar yadda shugaban masu rinjaye a majalisar Mitch McConnell ya sanar a makon da ya gabata.

Talla

Majalisar dattawan wadda magoya bayan jam’iyyar Republican ke da rinjaye a cikinta, ta fara muhawara kan wannan batu ne bayan majalisar wakilai inda Democrat ke da rinjaye ta amince da matakin tsige shugaba Trump.

Ana tuhumar Donald Trump da gayyatar Shugaban Ukraine na yi katsalandan a zabukan Amurka, da kuma amfani da karfin ikonsa ta hanyar da bata dace ba.

Wannan mataki da aka shiga, ya sanya Donald Trump zama shugaban Amurka na 3 a tarihi da zai gurfana gaban ‘yan majalisun kasar, bisa tuhumarsa da aikata laifukan da za su kai ga tsige shi daga karagar mulki.

Sai dai wasu magoya bayan shugaban harma da shi kansa, na ganin zai yi wahala matakin tsige shi ya kai ga samun nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.