Amurka-Najeriya

Dr Abdulrafiu Lawal kan matakin Amurka na hana kasashe 7 biza

Shugaban Amurka Donald Trump yayin jawabinsa a taron tattalin arziki na Davos.
Shugaban Amurka Donald Trump yayin jawabinsa a taron tattalin arziki na Davos. EUTERS/Jonathan Ernst

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirin sanya sunayen wasu karin kasashen da za’a takaitawa bai wa jama’arsu bizar shiga kasar, saboda abinda ya kira matakan kare Amurkawa.

Talla

Trump ya shaidawa taron tattalin arzikin da ke gudana a Davos cewar, nan bada dadewa ba za’a bayyana sunayen kasashen.

Sai dai tuni Jaridar Wall Street Journal ta bayyana kasashen guda 7 da suka hada da Najeriya da Eritrea da Sudan da Tanzania da Myanmar da Belarus da kuma Kyrgystan a matsayin wadanda ke iya fuskantar hanin bizar daga Amurka.

Dangane da wannan mataki, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dr Abdulrafiu Lawal, masanin siyasar Amurka, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.

Dr Abdulrafiu Lawal kan matakin Amurka na hana kasashe 7 biza

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.