Amurka-Faransa

Rage Sojin Amurka a Afrika zai haifar da matsalar tsaro- Parly

Ministar tsaron Faransa Florence Parly da takwaranta na Amurka Mark Esper a Washington.
Ministar tsaron Faransa Florence Parly da takwaranta na Amurka Mark Esper a Washington. OLIVIER DOULIERY / AFP

Ministar tsaron Faransa Florence Parly ta ce rage sojojin Amurka da ke aiki a nahiyar Afirka zai yi matukar illa wajen yaki da Yan ta’addan dake cin karen su babu babbaka.

Talla

Yayin ganawa da takwaranta Mike Esper a Washington, Parly ta ce gudumawar Amurka wajen yakin da Faransa ke yi da 'yanta’adda na da matukar muhimmanci, kuma rage sojojin zai shafi yakin.

Ministan ta ce kawayen Faransa da ke Yankin Sahel na matukar bukatar taimako, saboda haka yana da kyau kasashen biyu su cigaba da taimaka musu.

Sai dai Sakataren tsaron Amurka ya ce matakin rage sojojin zai shafi kasashen duniya ne baki daya, ciki harda Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.