Isra'ila-Falasdinawa

Kasashen duniya sun mayar wa Trump martani kan Isra'ila

Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a fadar White House
Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a fadar White House MANDEL NGAN / AFP

Kasashen duniya sun fara mayar da martini kan shirin shugaba Donald Trump na sasanta rikicin Gabas ta tsakiya tsakanin Israila da Falasdinawa, inda shugban ya jaddada cewa, birnin Kudus zai ci gaba da kasancewa karkashin cikakken ikon Isra'ila.

Talla

Shugaban Kungiyar Falasdinawa Mahmud Abbas ya bayyana shirin a matsayin abin da ba zai samu nasara ba, kuma za su yake shi ta kowacce hanya a cewarsa.

Majalisar Dinkin Duniya ta bakin Magatakardarta Antonio Guterres ta ce, har yanzu tana kan matsayin da ta dauka a shekarar 1967 dangane da kafa kasashen Isra'ila da Falasdinu akan iyakokinsu, sabanin sabon shirin shugaba Trump.

Kasashen Rasha ta hannun mataimakin Ministan Harkokin Wajenta Mikhail Bogdanov ta ce, za ta yi nazarin shirin, amma kuma ta bukaci Isra'ila da Falasdinawa da su tattauna a tsakaninsu.

Kasar Turkiya ta yi watsi da shirin gaba daya, inda ta ce shirin na dauke da ci gaba da mamaye yankunan Falasdinawa domin hana su samun kasa ta kansu.

Daular Larabawa wadda  ta aika wakilinta zuwa taron gabatar da shirin na Trump, ta yaba wa shirin nasa, yayin da Jordan ta ce, kafa kasar Falasdinu kan iyakokinta na shekarar 1967 ne kawai mafita.

Saudi Arabia ta yaba da matakin da Trump ya dauka, inda ta bukaci tattaunawar gaba da gaba tsakanin bangarorin biyu, yayin da Iran ta bayyana shirin a matsayin abin kunya.

Kungiyar Hezbollah ta bayyana shirin a matsayin yunkurin kawar da Falasdinawa daga doron kasa, yayin da Kungiyar Kasashen Turai ta ce, za ta yi nazari akai.

Firaministan Birtaniya, Boris Johnson ya ce, shirin na iya zama mataki mai muhimmanci, a daidai lokacin da Masar ke bukatar kyakyawar nazari akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.