Faransa-Turkiya

Macron da Erdogan sun yi musayar zafafan kalamai kan Libya

Shugaban Emmanuel Macron da takwaransa na Turkya Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban Emmanuel Macron da takwaransa na Turkya Recep Tayyip Erdogan. LUDOVIC MARIN / POOL / AFP

Ma’aikatar tsaron Faransa ta sanar da yadda wasu jiragen yakinta suka gano jerin gwanon manyan jiragen ruwan Turkiya na aikin dakon makamai baya ga motocin sulke zuwa Libya, duk kuwa da ikirarin shugaban Turkiya na cewa za su yi fatan yayyafawa rikicin na Libya ruwan sanyi ba tare da amfani da karfin Soji ba.

Talla

Ikirarin ma’aikatar tsaron ta Faransa na zuwa kwana guda bayan Turkiya ta zargi kasar da yunkurin katsalandan a harkokin tsaron Libya, zargin Macron ya ya ce Recep Tayyib Erdogan na kokarin boye ta’asar da ya ke shirin aikatawa a Libyan ne.

A cewar ma’aikatar tsaron Faransa, dankareren jirgin dakon kaya na Turkiya ya isa birnin Tripoli a shekaran jiya Laraba, makare da kayakin yaki ciki har da motoci masu sulke, matakin da shugaba Emmanuel Macron ke cewa, sun hannun riga da ikirarin shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan wanda ya sha alwashin sasanta rikicin kasar ba tare da amfani da karfin Soji ba.

Ka zalika Faransar ta bayyana isar kayakin yakin na Turkiya Libya a wani mataki da ya keta dokokin Majalisar Dinkin Duniya da ya haramtawa Libyan cinikin makamai bayan rikicin kasar da yak ai ga hambarar da gwamnati Mu’ammar Gaddafi.

Sai dai shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan da ke goyon bayan gwamnatin Firaminista Fayez al sarraj mai samun goyon bayan Majalisar dinkin duniya, ya ce kalaman na Macron na da nasaba da yadda Faransar ke bayar da cikakken goyon baya ga Khalifa Haftar mai rike da galibin sassan kasar ta Libya.

A cewar shugaba Erdogan baza su zuba ido Haftar ya ci gaba da farmaki tare da kame manyan yankunan kasar ba, yayinda ya bayyana Faransa a wadda ke fatan sake barkewar rikici a kasar, kuma wadda ke taimakawa Haftar hambarar da gwamnati a sirrance.

Wannan dai ba shi ne karon farko da shugaban na Faransa Emmanuel Macron ke musayar zafafan kalamai da shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiya ba, musamman kan al’amuran da suka shafi Syria da Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI