Falasdinawa sun yanke hulda tsakaninsu da Amurka da Isra'ila
Shugaban yankin Falasdinawa Mahmud Abbas ya sanar da yanke duk wata hulda tsakaninsu da Amurka da kuma Isra’ila.
Wallafawa ranar:
Abbas ya sanar da daukar matakin ne a Alkahira babban birnin Masar, bayan kammala taron kungiyar kasashen larabawa kan shirin zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar.
Matakin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan shirin zaman lafiyar gabat tsakiya ciki hardasasanta rikicin Falasdinawan da Isra’ila, da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a makon jiya.
Mintoci bayan gabatar da shirin ne kuma Falasdinawa suka yi watsi da shi, saboda karkatarsa wajen fifita Isra’ila.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu