Isa ga babban shafi
China

Kasashe na ci gaba da kauracewa China saboda annobar Corona

China's isolation grows as virus toll reaches 259. AFP / Anthony WALLACE
China's isolation grows as virus toll reaches 259. AFP / Anthony WALLACE AFP / Anthony WALLACE
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Kasashen duniya na ci gaba da kauracewa China ta hanyar dakatar da sufuri tsakaninsu da ita, sakamakon annobar murar mashako ta Corona dake cigaba da halaka rayuka a kasar, da kuma yaduwa zuwa wasu kasashen.

Talla

Adadin mutanen da annobar murar ta corona ta halaka a kasar ta China kadai ya kai 259, yayinda kuma annobar ta harbi wasu mutanen akalla dubu 11,791, abinda ya sanya Amurka da Australiada Vietnam dakatar da zirga-zirga tsakaninsu da kasar.

A kasashen ketare kuma kawo yanzu, hukumomin lafiyar Birtaniya, Rasha da kuma Sweden sun tabbatar da bullar annobar murar mashakon ta corona a kasashen, abinda ya kara adadin wadanda annobar ta bazu garesu zuwa akalla kasashe 24.

Ranar Juma'a hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana dokar-ta-baci kan annobar ta Coronavirus wadda ke ci gaba da yaduwa a wasu kasashen duniya.

Shugaban Hukumar Lafiyar ta WHO, Tedros Adhanom Ghebreysus ya ce, babban makasudin ayyana dokar ta bacin kan cutar Coronavirus a duniya, ba wai don abin da ke faruwa a China ba ne, illa don abin da ke faruwa a wasu kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.