Gabas ta Tsakiya

Kasashen Larabawa sun yi fatali da shirin zaman lafiyar Trump

Taron ministocin harkokin wajen kasashen larabawa a Alkahira babban birnin kasar Masar, kan shirin zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya da shugaba Trump ya gabatar.
Taron ministocin harkokin wajen kasashen larabawa a Alkahira babban birnin kasar Masar, kan shirin zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya da shugaba Trump ya gabatar. Reuters

Kungiyar kasashen larabawa ta yi fatali da shirin zaman lafiya ko sasanta rikicin yankin gabas ta tsakiya da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar a makon jiya.

Talla

Kasashen sun bayyana matsayar su kan shirin ne bayan taron gaggawar da suka yi ranar asabar a Masar, inda suka bayyana shirin mai shafuka 80 a matsayin abu mai kunshe darashin adalci ga Falasdinawa.

Daga cikin abinda shirin zaman lafiyar ya kunsa akwai, fayyace iyakokin kasashen biyu dake bayyana cewar Israila zata mallake Yankunan Falasdinawa 15 da ta gina gidajen da Yahudawa ke ciki, wadanda akewa lakabi da Yankunan ‘Yan kama wuri zauna.

Tuni dai shugaban yankin Falasdinawa Mahmud Abbas ya sanar da yanke duk wata hulda tsakaninsu da Amurka da kuma Isra’ila, a dalilin rashin adalcin da ya ce na tattare cikin shirin sasanta rikicinsu da Amurkan ta gabatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.