Isa ga babban shafi
Amurka

Democrat na dab da tsayar da dan takarar da zai kara da Trump

Masu neman Jam'iyyar Democrat ta tsayar da su domin karawa da shugaba Donald Trump na Amurka a zabe mai zuwa
Masu neman Jam'iyyar Democrat ta tsayar da su domin karawa da shugaba Donald Trump na Amurka a zabe mai zuwa Charlie Neibergall/AP

'Yan Jam’iyyar Democrat a Amurka sun fara gudanar da zaben fid da gwanin dan takarar da zai fafata da shugaba Donald Trump a zabe mai zuwa, sai dai rashin gabatar da sakamakon zaben da aka yi a Jihar Iowa ya haddasa rudani.

Talla

Zaben na Iowa na da matukar tasiri ga 'yan sahun gaba daga 'yan takarar da suka hada da Sanata Bernie Sanders da tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden.

Daraktan sadarwar Jam’iyyar Democrat a Iowa, Mande McClure ya ce, an bada umurnin sake tantance kuri’un da aka kada ne domin tabbatar da sahihancinsu kafin gabatar da sakamako.

Bayanai na cewa,tangardar na'ura ce ta haddasa rudanin, yayin da magoya bayan jam'iyyar sama da dubu 1 da 600 suka yi dafifi a makarantu da dakunan karatu da kuma coci-coci domin neman sanin sakamakon zaben a yau Litinin.

Duk da cewa, ba a sanar da sakamakon ba, da dama daga cikin 'yan takara sun yi ikirarin samun nasara a zaben na fid da gwani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.