Turkiya

Fasinja 177 sun tsallake rijiya da baya a hadarin jirgin Turkiya

Babu rahoton rasa rai a hadarin jirgin sai dai an samu adadi mai yawa na wadanda suka jikkata.
Babu rahoton rasa rai a hadarin jirgin sai dai an samu adadi mai yawa na wadanda suka jikkata. REUTERS/Murad Sezer

Wani Jirgin sama mai dauke da fasinja 177 ya zarce hanyar saukar sa a tashar jiragen saman birnin Santanbul da ke Turkiya inda jirgin ya rabu zuwa gida 3 a kokarinsa na tsayawa, ko da dai babu asarar rai.

Talla

Hukumomin kasar sun ce babu koda mutum guda da ya mutu sakamakon hadarin, sai dai tarin mutane sun samu raunuka daban daban.

Tashar talabijin din Turkiya ta nuna yadda fasinjojin jirgin suka yi ta haura buraguzan sa suna ficewa domin tsira da rayukan su.

Rahotanni sun ce jirgin kirar Boeing 737 mallakar kamfanin Pegasus ya tashi ne daga tashar Izimir zuwa Santanbul, yayin da ya yi fama da matsalar ruwan sama da iska lokacin saukar sa.

Gwamnan Santanbul Ali Yerlikaya ya ce mutane 52 sun samu raunuka kuma ana kula da su a asibiti, yayin da kafofin yada labaran Turkiya suka ce matuka jirgin biyu, dan kasar Turkiya da dan kasar Koriya ta kudu sun samu raunuka sosai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.