MDD

'MDD na nan daram kan kudirinta na Falasdinu'

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres REUTERS/Brendan McDermid

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce, hakkin Majalisar ne ci gaba da kare dokokin duniya a rikicin da ke gudana tsakanin Israila da Falasdinu, kwanaki kalilan da shugaba Donald Trump na Amurka ya gabatar da shirins na sasanta rikicin bangarorin biyu.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai Guterres ya ce, matsayin Majalisar Dinkin Duniya a fayyace yake dangane da dokokin duniyar da kuma matsayin Falasdinu.

Guterres ya ce, har yanzu babu abin da ya sauya dangane da matsayinsu na samun kasashe biyu tsakanin Israila da Falasdinu a kan iyakokin shekarar 1967.

Wannan matsayi na Guterres da Majalisar Dinkin Duniya ya ci karo da shirin shugaba Trump wanda ya mallaka wa Israila Birnin Kudus da kuma halarta mata mamaye wasu yankuna da suka hada da tuddan Golan da Yankin Jordan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.