Duniya

Kwari rabin milyan ke fuskantar barazanar bacewa

Bacewar kwari na barazana ga zaman lafiyar dan Adam a bayan kasa
Bacewar kwari na barazana ga zaman lafiyar dan Adam a bayan kasa Jimini's

Masana Kimiya sun bayyana cewar yanzu haka akalla dabbobi da tsirai 500,000 ke fuskantar barazanar bacewa daga doron kasa, cikin su harda kwari, kuma bacewar su zai zama babban bala’i ga Bil Adama.

Talla

Pedro Cardoso, masanin halitta a Finland, wanda ya jagoranci wani nazarin binciken da aka gudanar yace bacewar kwarin na barazana ga zaman lafiyar dan Adam a bayan kasa.

Cardoso ya bayyana ayyukan da Bil Adama keyi a matsayin dalilin bacewar kwarin, musamman wajen gurbata muhalli da kuma amfani da magungunan dake hallaka su.

Jami’in ya kuma ce daga cikin dalilan bacewar harda yadda mutane ke cin wasu daga cikin nauyin kwarin, wadanda suka hada da kuda da kiyashi da tururuwa da zuma da makamantar su.

Wani rahotan Majalisar Dinkin Duniya yace tsiran dake bukatar irin wadannan kwari wajen haihuwa na iya samar da tsakanin Dala biliyan 235 zuwa 577 kowacce shekara.

Masana kimiya sun bayyana cewar akwai akalla nauyin kwari sama da miliyan 5 a duniya, amma kuma kasha daya bisa biyar ne kawai aka iya tantancewa da kuma bada sunayen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.