Isa ga babban shafi
Syria-Turkiya

Turkiya ta kashe sojojin Syria 101

Yankin Idlib na kasar Syria
Yankin Idlib na kasar Syria AFP Photos/Omar Haj Kadour
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 1

Turkiya ta kashe sojojin Syria 101 bayan wani kazamin harin da suka kai wanda ya kasha mata sojoji 5 a Yankin Idlib. Ma’aikatar tsaron Turkiya tace bayan kasha sojojin Syria sama da 100 sun kuma lalata tankunan yakin kasar guda 3 da wasu manyan makamai guda 2.

Talla

Ko a makon jiya sanda an fuskanci takun saka tsakanin bangarorin biyu, lokacin da dakarun Syria suka kai hari matsugunin sojin Turkiya dake Idlib, matakin da ya haifar da martani mai zafi daga Turkiyar.

Masu sa ido kan rikicin Syria na fadin cewar, babakeren da sojin Turkiya suka yi a cikin kasar na iya haifar da yaki a tsakanin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.