Rasha-Turkiya-Syria

Rasha ta zargi Turkiya ta gaza cika alkawarin fatattakar 'yan tawayen Syria

Shugaban Rasha Vladimir Putin da Recep Tayyib Erdogan na Turkiya.
Shugaban Rasha Vladimir Putin da Recep Tayyib Erdogan na Turkiya. Maxim Shipenkov/Pool via REUTERS

Rasha ta zargi Turkiya da gaza kawo karshen kungiyoyin ‘yan ta’adda a lardin Idlib, yanki na karshe kuma mafi girma da ke karkashin ikon ‘yan tawayen Syria.Kakakin shugaban Rasha Dmitry Peskov ne ya soki Turkiya yayin tsokaci kan yarjejeniyar da suka cimma a shekarar 2018.

Talla

Yayinda ya ke caccakar Turkiya, Dmitry Peskov ya yi tir da yadda kasar ta saba alkawarin da ta dauka bisa radin kanta, yayin cimma yarjejeniyar samar da yankin tudun mun tsira a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin Syria cikin shekarar 2018 a birnin Sochi, inda kasar ta Turkiya ta sha alwashin murkushe duk wata kungiyar ‘yan ta’adda da ke fakewa a yankunan da ‘yan tawaye ke iko da su.

Sai dai kakakin gwamnatin Rashan ya ce bayan shafe shekaru 2, a maimakon kawo karshen ‘yan ta’addan sai ma karfinsu da ya karu, inda a yanzu haka suke kaiwa sojojin Syria munanan hare-hare da kuma kaiwa muradun Rasha hare-hare a sassan kasar ta Syria.

A gafe guda kuma, Rasha ta kare sojojin gwamnatin Syria kan farmakin da suka kaddamar a baya bayan nan a lardin Idlib, wadanda ta ce sun mayar da da hankali kan ‘yan ta’adda, a maimakon fararen hular da ake zargin suna ci gaba da yiwa kisan gilla.

A larabar nan shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya yi barazanar kai wa sojin Syria farmaki, muddin aka sake kai musu hari, inda kuma ya zargi Rasha da aikata kisan kare dangi a lardin Idlib.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.