AMurka- Falasdinu

'Shirin Trump zai dagula lissafi a gabas ta tsakiya'

Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas.
Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas. REUTERS/Shannon Stapleton

Shugaban Falasdinu Mahmud Abbas ya shaida wa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa shirin sulhu a Gabas ta Tsakiya da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar, zai kara dagula lissafi ne kawai.

Talla

A cewar shugaban Falasdinun, tsarin da Trump ya gabatar zai cutar da Falasdinawa ne kawai, domin babu yadda zai kawo zaman lafiya da tsaro a gabas ta tsakiya.

A cewar Abbas tsarin ya share dukkan hakkokin Falasdinawa na kasancewa kasa mai cin gashin kanta, kamar Isra'ila.

Ya ce, samun sulhu da Isra'ila abu ne mai yiwuwa idon akwai adalci, sabanin yadda da farko yake kallon Trump da zaton zai yi adalcin.

Falesdinawa dai na kara neman goyon bayan duniya ne don adawa da tsarin shugaba Trump na Amurka, wanda ya gabatar tare da shugaban Israiila Benjamin Netanyahu.

Karkashin tsarin na Trump dai, Isra'ila ta samu amincewar handame wuraren da ake takaddama akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.