Isa ga babban shafi
China

China ta kori 'yan siyasa saboda sakacin kula da lafiyar jama'a

Shugaban China Xi Jinping na ran gadi a wuraren yaki da cutar Coronavirus
Shugaban China Xi Jinping na ran gadi a wuraren yaki da cutar Coronavirus ©Xinhua via REUTERS
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

A yayin da sabuwar cutar COVID-19 da aka fi sani da Coronavirus ta kashe mutane sama da dubu 1 da 360, gwamnatin China ta kori wasu manyan 'yan siyasa a lardin Wuhan da Hubei sakamakon sakacinsu wajen tunkarar cutar.

Talla

Kasar China ta bayar da rahoton sabbin mutane 242 da suka mutu a sanadiyar Coronavirus, yayin da cutar da sake harban mutane dubu 14 da 840 a Hubei, kuma an samu wadannan alkaluma ne a kwana guda.

A jumulce dai, cutar ta kama mautane sama da dubu 60, sannan ta lakume rayuka kusan dubu 1 da 400 a China kadai, yayin da mahukuntan China suka kori manyan shugabannin siyasa saboda yadda suka gaza tunkarar annubar.

Kazalika an sallami babban jami’in Kungiyar Agaji ta Red Cross a Wuhan sakamakon sakaci da aikinsa, sai kuma wasu jami’an kiwon lafiya da dama da su ma aka tube su a wasu biranen China.

A bangare guda, Vietnam ta zama kasa ta farko a duniya baya ga China da ta kaddamar da gagarumin aikin killace tarin al’umma domin yi musu gwajin Coronavirus , inda aka kebe sama da mutane dubu 10 a wasu kauyuka shida don sanya ido akan su cikin kwanaki 20.

Kazalika gwaji ya nuna cewa, mutane 44 da aka killace a jirgin yawon budo ido a gabar ruwan Japan, sun kamu da cutar.

Har ila yau, wannan annuba ta tilasta soke guadnar da babban bikin baje kolin wayoyin tarho na duniya da aka shirya gudanarwa a birnin Barcelona a cikin wannan wata na Fabairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.