Majalisar Amurka ta hana Trump kai wa Iran hari
Wallafawa ranar:
Majalisar Dattawan Amurka ta kada kuri’ar haramta wa shugaba Donald Trump kai wa Iran hari, kudirin da ya samu goyan bayan 8 daga cikin 'yan jam’iyyarsa ta Republican.
A karkashin wannan doka, shugaba Donald Trump ba shi da hurumin kai wa Iran hari ba tare da neman izini daga Majalisar ba wadda kundin tsarin mulki ya ba ta hurumin amincewa kan ko Amurka ta shiga yaki ko kuma a’a.
'Yan Majalisu 55 suka amince da kudirin, yayin da 45 suka ki.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Amurka fiye da 100 suka samu rauni a kwakwaluwarsu sakamakon harin ramuwar gayya da Iran ta kaddamar kan sojin na Amurka a Iraqi.
Amurka ce ta fara kai harin da ya yi sanadiyar mutuwar babban kwamandan sojin Iran, Qassem Soleimani a Irqi, al'amarin da Iran ta lshi takobin daukar fansa a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu