Syria-Turkiya

Syria ta tuhumi Turkiya da yiwa 'yan Armeniya kisan kiyashi

Wasu Armeniyawa a birnin Aleppo kafin barkewar yakin Syria.
Wasu Armeniyawa a birnin Aleppo kafin barkewar yakin Syria. AFP

A wani mataki na maida martani kan hare haren da Turkiya ke kaiwa kan sojojin kasarta, Majalisar dokokin Syria ta kada kuri’ar tuhumar Turkiya da aikata kisan kiyashi kan Armeniyawa miliyan 1 da dubu 500 a tsakanin shekarun 1915 zuwa 1917.

Talla

Majalisar dokokin kasar ta Syria ta ce Turkiya ta aikata kisan kiyashin ne karkashin daular Ottoman a farkon karni na 20.

Mahukumtan Erevan baban birnin kasar Armeniya dai, na zargin gwamnatin Ottoman da tisa keyar dubban Armeniyawa zuwa Syria, wadanda ta halaka mafi akasarinsu, wadanda suka tsira da rayukansu kuma, ta killace su a wasu sansanoni dake yankin arewa maso yammaci da kuma gabashin kasar ta Syria.

A ranar larabar da ta gabata shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi barazanar kai hare hare ta ko ina a kan Syria, idan har dakarun kasar suka sake kaiwa sojojinsa farmaki, wadanda ya tura yankin arewacin ta kasar da sunan kare kan iyakokinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.