Iraq-Amurka

An kai hari a harabar ofishin jakadancin Amurka

Harabar ofishin jakadancin Amurka a Iraqi
Harabar ofishin jakadancin Amurka a Iraqi REUTERS/Thaier al-Sudani

An kai jerin hare-hren makaman roka a kusa da ofishin jakadacin Amurka da ke babban birnin Iraqi a sanyin safiyar yau Lahadi, harin da shi ne na baya-bayan nan da aka kai kan kadarar Amurka da ke kasar.

Talla

Rundunar hadakar ta tabbatar da farmakin kan sansanin da ke dauke da dakarun Amurka a kusa da ofishin jakadancin kasar a birnin Bagadaza.

Sansanin shi ne shalkwatan rundunar da Amurka ke jagoranta a yaki da kungiyar ISIS,  yayin da ake zargin mayakan Hashed al-Shaabi da kai farmakin na yau.

Kawo yanzu babu bayani game da rasa rai ko kuma jikkata, amma wannan harin shi ne na 19 tun daga watan Oktoba da aka kaddamar da zummar lahanta ofishin jakadancin Amurka ko kuma dakarun kasar kimanin dubu 5 da 200 da ke Iraqin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.