China-Corona

Coronavirus ce kalubale mafi girma a gare mu- Xi Jinping

Shugaban China Xi Jinping rufe da hanci da baki saboda fargabar kamuwa da cutar Coronavirus
Shugaban China Xi Jinping rufe da hanci da baki saboda fargabar kamuwa da cutar Coronavirus Tân Hoa Xã/ Reuters

Shugaban China Xi Jinping ya bayyana cutar Coronavirus da ta kashe mutane sama da dubu 2 da 590, a matsayin kalubale mafi girma da kasar ta fuskanta a bangaren kiwon lafiya tun shekarar 1949.

Talla

A wani taron hukumomi kan tsara yaki da Coronavirus, shugaban China ya ce, dole ne su dauki darasi daga gagarumin kuskuren da kasar ta tafka wajen tunkarar cutar cikin hanzari, kalaman da ba kasafai wani shugaba a China ke furta su ba.

Shugaba Xi ya kara da cewa, cutar ta Coronavirus na yaduwa cikin gaggawa, sannan tana mamaye wurare da dama, yayin da ta kasance mai wuyar sha’ani wajen dakile ta.

A cewar shugaban, wannan tashin hankali ne da ya shafe su baki daya kuma wani imtihani ne.

Duk da cewa, Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta jinjina wa China kan yadda ta dauki matakan yaki da cutar, amma mutuwar Likitan nan da ya fara fallasa cutar wato Li Wengliang, ta tunzura kiraye-kirayen samar da sauyi a fagen siyasar China da kuma fadin albarkacin baki.

Mahukuntan China sun tsare wannan likitan bayan ya yi gargadi kan bullar cutar.

A halin yanzu dai, Coronavirus ta harbi mutane kimanin dubu 77 a cikin kwaryar China kadai, inda kuma kasashe irin su Koriya ta Kudu da Italiya suka kasance cikin gagarumin shirin ko-ta-kwana tare da daukar matakan tunkurar annubar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.