India

Kisan Musulmi ya zama ruwan dare a India- Erdogan

Kimanin mutane 33 suka mutu a rikicin addini a India
Kimanin mutane 33 suka mutu a rikicin addini a India REUTERS/Danish Siddiqui

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da mabiya addinin Hindu ke yi wa al’ummar Musulmi a rikicin da ke gudana a birnin Delhi wanda tuni ya yi sanadiyar mutuwar mutane 33.

Talla

Yayin da ya ke jawabi a Ankara, Erdogan ya bayyana India a matsayin kasar da kisan Musulmi ya zama ruwan-dare, ganin yadda mabiya Hindu ke afka wa Musulmi saboda korafin da suke yi kan sabuwar dokar zama dan kasa.

A kalla mutane sama da 200 suka samu raunuka, yayin da 33 suka mutu tun bayan barkewar rikicin wanda ya fara a daidai lokacin da shugaba Donald Trump na Amurka ke ziyarar kasar.

Fitaccen mai wa’azin Musuluncin India, Dr Zakir Naik ya bukaci kasashen Musulmi da Majalisar Dinkin Duniya da su daga muryarsu wajen ganin an kawo karshen wannan kisan gillar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.