Isra'ila

Netanyahu ya sha alwashin mamaye yankunan Falasdinawa

Firaministan Israila Benjamin Netanyahu yace da zaran yayi nasarar zaben da za’ayi gobe litinin zai fara aiwatar da shirin mamaye yankunan Falasdinawa dake gabar Yamma da Kogin Jordan.

Fira Minista mai ci Benjamin Netanyahu, a lokacin da yake alkawarin mamaye yankunan Falesdinawa
Fira Minista mai ci Benjamin Netanyahu, a lokacin da yake alkawarin mamaye yankunan Falesdinawa Debbie Hill/Pool via REUTERS
Talla

Netanyahu dake neman goyan baya masu kada kuri’u ganin yadda ya kasa kafa gwamnati sau biyu yace abinda ke gaban sa shine mamaye tsaunukan Jordan da kuma wani sashe na Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Kuri’un jin ra’ayin jama’a sun nuan cewar har yanzu Netanyahu da Janar Benny Gantz na tafiya kan kan kan ba tare da samun wanda yayi rinjaye ba, duk da shirin gurfanar da Netanyahu a kotu kan zargin almundahana da cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI