Coronavirus ta lakume sabbin rayuka a Iran da Amurka
Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a sassan duniya a sanadiyar cutar Coronavirus ya haure dubu 3, yayin da cutar ta lakume sabbin rayuka a China da Iran da kuma Amurka. Annubar na ci gaba da bazuwa a kasashen duniya.
Wallafawa ranar:
Kwayar cutar Coronavirus ta harbi mutane fiye da dubu 89 bayan ta bazu a kasashen duniya sama da 60 tun daga lokacin da ta fara bulla a China a karshen shekarar bara.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukaci ilahirin kasashen duniya da su kara kaimi wajen tanadar hanyoyin samun iska ga marasa lafiyar da suka nuna alamun kamuwa da cutar murar mashakon mai kisa.
Bazuwar cutar kamar wutar daji ta haifar da nakasu ga tattalin arzikin duniya, inda Hukumar Tattalin Arziki ta Kasa da Kasa, OECD ta rage hasashenta na babbakar tattalin arzikin duniya zuwa kashi 2.4, alkaluma mafi muni da aka gani tun shekarar 2008 zuwa 2009.
Tuni tattalin arzikin China, inda wannan cuta ta samo asali, ya yi kasa warwas, lura da cewa, an killace yankuna da dama na kasar tare da takaita zirga-zirgar jama’a.
Ko a wannan Litinin sai da kasar China ta bayar da rahoton sabbin mutane 42 da Coronavirus ta kashe a lardin Hubei.
Alkaluman mamatan ya kai dubu 2 da 912 a China kadai, sannan ana ci gaba da samun asarar rayuka a wasu kasashen duniya a sanadiyar cutar, inda a Iran aka samu karin mutane 12 da suka mutu a yau. Sai kuma Amurka ta mutun guda ya sake shekawa lahira a Washington.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu