Coronavirus

Kasashe na cigaba da dauki-ba-dadi da annobar Coronavirus

Adadin mutanen da annobar Corona ta halaka a Iran ya zarta na kowace kasa banda kasar China, inda cutar ta soma bulla.
Adadin mutanen da annobar Corona ta halaka a Iran ya zarta na kowace kasa banda kasar China, inda cutar ta soma bulla. AFP Photo/ATTA KENARE

Adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon kamuwar da kwayar cutar Corona ya zarta dubu 3 a sassan duniya, yayin da a yau litinin aka samun karin mutane 42 da suka mutu sakamakon cutar a kasar China kawai.

Talla

Sabbin alkaluma da aka fitar a safiyar yau litinin, na tabbatar da cewa a kasar China kawai, adadin wadanda ke dauke da kwayar cutar sun haura dubu 80 yayin da tuni 2,912 suka rasa rayukansu.

Kasa ta biyu da annobar Coronar tafi shafa bayan China ita ce Koriya ta Kudu, inda sabbin alkaluman ke nuni da cewa masu dauke da ita sun kai dubu 4 da 212 tare da asarar rayukan mutane 22.

A kasar Iran duk da cewa adadin wadanda suka kamu da cutar har yanzu bai kai dubu daya ba, zuwa safiyar wannan litinin adadin mamata ya kai 54.

A yankin Turai kuwa har zuwa wannan lokaci a Italiya cutar ta fi yaduwa saboda yawan masu dauke da ita ya kai dubu 1 da 694 tare da asarar rayuka 34.

A Amurka mutuum na biyu ya mutu sakamakon cutar, yayinda a Faransa aka rufe wasu muhimman wuraren taruwar jam’a ciki har a gidan ajiye kayayyakin tarihi mafi girma a duniya wato Louvre da ke Paris, yayinda mahukuntan kiwon lafiya a kasashen Algeria, Masar da kuma Najeriya da ke da mutum dai dai da ya kamu da kwayar cutar ke ci gaba da kokarin hana yaduwarta tsakanin al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.