najeriya - coronavirus

Coronavirus ta rubanya a duniya-WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya, ta ce yanayin da kwayar cutar Coronavirus ke yaduwa a duniya ya rubanya har sau 9 cikin sa’o’i 24, duk da cewa an samu karancin yaduwarta a kasar China inda ta samo asali. Yanzu haka dai an samu karin kasashe uku a nahiyar Afrika da cutar ta bulla.

Wasu daga cikin jami'an yaki da Coronavirus
Wasu daga cikin jami'an yaki da Coronavirus Yonhap via REUTERS
Talla

Sabbin kasashen da aka tabbatar da bullar Coronavirus a nahiyar Afrika su ne Senegal da Tunisia da kuma Moroko, abin da ke nuni da cewa a yanzu kasashe 6 ne ke fama da cutar a nahiyar.

Ministan Kiwon Lafiyar Senegal Diouf Sarr ya ce, wanda aka samu dauke da kwayar cutar wani Bafaranshe ne da ya dawo daga hutu a tsakiyar watan Fabarairun da ya gabata kuma tuni aka killace shi a wani asibiti da ke birnin Dakar.

A can Moroko kuwa, wanda ya kamu da cutar dan asalin kasar ne da bai jima da dawowa daga kasar Italiya ba, yayin da a Tunisia ma kusan haka lamarin yake, domin kuwa a cewar ministan lafiya Abdellatif Mekki, tabbas wanda ke dauke da kwayar cutar dan kasar ne da bai da dawowa daga Italiya.

A can ma kasar China, cikin sabbin mutane da suka kamu da cutar a baya-bayan nan, hukomomin kiwon lafiya sun ce, 7 daga cikinsu sun shiga kasar ne daga Italiya.

Wasu daga cikin sabbin kasashen da cutar ta bulla tsakanin jiya zuwa yau sun hada da Jamhuriyar Czech, Indonesia, Jordan, Latvia, Portugal, da kuma Saudiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI