Jirgin Amurka mara matuki ya rikito a Nijar

Rundunar Sojin Amurka ta ce, wani jirginta mai sarrafa kansa ya fadi a Agadez na Jamhuriyar Nijar sakamakon matsalar inji.

Samfurin jirgin Amurka mara matuki
Samfurin jirgin Amurka mara matuki theaviationist
Talla

Sanarwar da rundunar ta bayar ta ce, a ranar Asabar da ta gabata ne jirgin ya fadi lokacin da yake gudanar da aikinsa a yankin Agadez kuma binciken da suka yi ya tabbatar musu cewar matsalar inji ya samu.

Wannan shi ne jirgi na biyu da Amurka ke amfani da shi ya lalace a Nijar, bayan wanda ya fadi a tashar jiragen saman Yammai, abin da ya sa aka rufe tashar na wani lokaci.

Kasar Amurka ta fara amfani da jirgin sama mai sarrafa kansa wajen tara bayanan asiri da kuma yaki da ‘yan ta’adda daga Nijar a shekarar 2013, ganin yadda suka addabi arewacin kasar Mali.

Jamhuriyar Nijar ta bai wa Amurka damar gina tashar samar da jiragen a Agadez da kuma sa ido kan yankin Sahel gaba daya.

A shekarar da ta gabata, sojojin Amurka sun fara amfani da sansanin Dirkou da ke kusa da Libya wajen harba ire-iren wadannan jirage.

Ita ma kasar Faransa na da sansanin a tashar jiragen saman Yammai inda take amfani da shi wajen tashin jiragenta na yaki domin kai hari kan ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI