Trump ya zanta da shugaban Taliban

Shugabannin kungiyar Taliban lakacin da suka taro gabanin tattaunawar su da Amurka
Shugabannin kungiyar Taliban lakacin da suka taro gabanin tattaunawar su da Amurka REUTERS/Ibraheem al Omari

Shugaban Amurka Donald Trump ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kungiyar mayakan Taliban dake Afghanistan Mullah Baradar kwanaki bayan kasar ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar.

Talla

Trump dake ganawa da manema labarai a Washington ya tabbatar da tattaunawar da ya yi amma ba tare da bayyana sunayen wadanda ya yi Magana da su ba.

Mai Magana da yawun kungiyar Taliban ya ce Talatan nan akayi tattaunawar ta mintina 35 ta waya tsakanin shugabannin biyu da misalin karfe 2 da minti 20 agogon GMT.

Fassarar kalaman ganawar da akayi ta bayyana yadda shugabannin suka mayar da hankali kan janyewar sojin Amurka daga Afghanistan kamar yadda bangarorin biyu suka amince.

Yarjejeniyar ta kunshi sakin firsinonin da Taliban ke rike da su da kuma sakin Yan Taliban 5,000 dake hannun gwamnati a matsayin daya daga cikin sharuddan da zasu tattauna da gwamnatin Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.