Amurka

Biden ya bada mamaki a zaben Amurka

Joe Biden
Joe Biden MARIO TAMA / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

Tsohon mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden ya lashe jihohi 9 daga cikin jihohi 14 da suka kada kuri’a a zaben Super Tuesday domin fid da dan takarar Jam’iyyar Democrat.

Talla

Biden ya bada mamaki ganin yadda ya sha gaban babban abokin takararsa, Bernie Sanders a jihar Texas mai muhimmanci.

Sai dai ana hasashen cewa, Mr.Sanders zai yi nasara a California da kuma wasu karin jihohi uku.

‘Yan takarar biyu na kan gaba wajen neman tikitin fafatawa da shugaba Donald Trump a zaben shugaban kasa da za a gudanar a cikin watan Nuwamba mai zuwa.

Tsohon Magajin Garin Birnin New York, Michael Bloomberg ya kashe fiye da rabin Dala biliyan 1 a yakin neman zabensa, amma bai lashe jiha ko daya ba.

Sauran jihohin da Biden ya lashe sun hada da Massachusetts da Minnesota da Oklahoma da Arkansas da Alabama da Tennessee da North Carolina da Virginia.

Biden, tsohon mataimakin Barrack Obama, ya samu goyon bayan dimbin Amurkawa bakaken fata da ke da tushen Afrika..

Sai dai ana ganin muddin Sanders ya lashe California, hakan zai ba shi damar samun kaso mafi tsoka a zaben na Super Tuesday, abin da zai kasance koma-baya ga Biden.

Sanders ya kuma lashe jiharsa ta Vermont da Colorado da kuma Utah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.