Coronavirus ta lakume sabbin rayuka a China da Amurka
A yau Laraba kasar China ta sanar da sabbin mutane 38 da cutar Coronavirus ta kashe duk da cewa, an samu raguwar yaduwar cutar cikin kwanaki uku a jere.
Wallafawa ranar:
A jumulce dai, mtane 2,981 ne Coronavirus ta kashe a China kadai kamar yadda Hukumar Lafiyar Kasar ta bayyana, sannan fiye da dubu 80 da 200 sun kamu da annubar.
Kodayake a ‘yan kwanakin nan, an samu sassaucin yaduwar cutar sakamakon kwararan matakan killace jama’a da gwamnatin China ta dauka.
Sai dai har yanzu, ana ci gaba da dari-darin cewa, baki daga wasu kasashen ketare ka iya dakon cutar daga wasu wurare zuwa cikin China.
A bangare guda, Amurka ta daura damarar jan ragama wajen fatattakar wannan annuba daga doran-kasa musamman ganin yadda take barazana ga tattalin arzikin duniya.
A halin yanzu, Amurkawa guda 9 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon annubar, sannan fiye da 100 sun kamu da ita a kasar.
Shi ma Bankin Duniya ya kaddamar da tallafin Dala biliyan 12 domin agaza wa kasashen da cutar ta yi wa dirar mikiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu