Coronavirus

Coronavirus ta tilastawa dalibai sama da miliyan 290 zama a gida

Sama da dalibai miliyan dari 290 ne matakin rufe makarantu na wucin gadi ya shafa a fadin duniya, saboda fargabar ci gaba da yaduwar annobar murar Coronavirus.

Kasashe 13 sun rufe makarantunsu saboda fargabar yaduwar annobar murar Coronavirus.
Kasashe 13 sun rufe makarantunsu saboda fargabar yaduwar annobar murar Coronavirus. REUTERS
Talla

Italiya da Iran ne kuma kasashen da a baya bayan nan suka dauki matakin rufe makarantun saboda annobar.

Hukumar kyautata ilimi da kimiya da raya al'adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO ta ce kasashe 13 ne yanzu haka suka rufe makarantunsu, ko dai baki daya ko kuma a wasu sassa, don dakile yaduwar wannan annoba, ciki kuwa har da Italiya, Korea ta Kudu, Japan, Iran da kuma Faransa.

A Italiya an rufe ilahirin makarantu da Jami’o’in kasar har zuwa 15 ga watan Maris da muke ciki, bayan da annobar murar ta halaka mutane 107, sai kuma Korea ta Kudu da ta dage cigaban zangon karatun bana zuwa 23 ga watan na Maris. A Iran ma haka abin yake sai dai wa’adin rufe makarantun kasar zai kai har cikin watan Afrilu.

A Japan kuma kusan baki dayan makarantun da jami’o’I aka rufe har sai farkon watan Afrilu, yayinda a Faransa matakin ya shafi makarantu 120 a yankunan Morbihan dake arewacin kasar da kuma arewacin birnin Paris.

Alkalumman hukumomin lafiya sun nuna cewar a halin da ake ciki sama da mutane dubu 95 ne suka kamu da annobar murar ta Coronavirus, yayinda kuma ta halaka wasu sama da dubu 3 da 300 a sassan duniya. Zalika zuwa yanzu annobar murar ta bulla a kasashe da manyan yankuna akalla 80.

Sama da kashi 90 na wadanda annobar Coronavirus din ta halaka a kasar China ne, inda ta bulla a karshen shekarar bara, abinda ya tilasta rufe masana’atu da makarantu har sai abinda hali yayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI