Syria

Erdogan da Putin sun gana kan rikicin Syria

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Turkiya Racip Tayip Erdogan
Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Turkiya Racip Tayip Erdogan Sputnik/Alexei Druzhinin/Kremlin via REUTERS

Shugabannin Rasha da Turkiya sun gana a birnin Moscow a daidai lokacin da ake fargabar barkewar rikici tsakanin dakarun kasashen biyu a Syria.

Talla

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan na fatan takwaransa na Rasha, Vladimir Putin zai amince a gaggauta tsagaita musayar wuta a yankin Idlib na Syria, inda sojojin Turkiya ke fada da dakarun da ke samun goyon bayan Rasha.

A jawabin bude tattaunawar ta yau a birnin Moscow, shugaba Erdogan ya bayyana cewa, daukacin al’ummar duniya sun zura musu ido, yana mai jaddada cewa, akwai bukatar samar da sassauci a yankin arewacin Syria.

Shugaba Putin ya ce, al’amura sun rincabe a Idlib, a don haka lokacin tattaunawar keke da keke a tsakaninsu ya yi.

Putin ya ce, akwai bukatar su tattaunawa kan komai don ganin cewa, wani abu bai sake faruwa ba nan gaba ballantana alakar da ke tsakanin Turkiya da Rasha ta sukurkuce baki daya .

Gomman sojojin Turkiya sun kwanta dama a ’yan kwanakin nan a sanadiyar rikicin yankin Idlib, yayin da a karon farko ta ta kaddamar da hari kai tsaye kan dakarun shugaba Bashar al’Assad na Syria.

Ana fargabar wannan rikicin zai haddasa mummunar kwararar ‘yan gudun hijira a Turai da kuma fito-na-fito tsakanin Rasha da Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI