Halin da ake ciki dangane da Coronavirus a duniya

Wasu fasinjoji sanye da kariyar baki da hanci a kasar Indonessia saboda Coranavirus
Wasu fasinjoji sanye da kariyar baki da hanci a kasar Indonessia saboda Coranavirus REUTERS/Johannes P. Christo

Yanzu haka Cutar murar Mashako ta Coronavirus ta kashe mutane 3,404 a duk fadin duniya, yayin da mutane kimanin 99,464 suka kamu da cutar ta nunfashi a kasashe 89, kamar yadda zabon kiddigar kamfanin dillancin labaran faransa AFP ya byyana yau Jumma’a.

Talla

Manyan kasashen da annobar Cutar murar mashako ta CoronaVirus tafi shafa baya ga kasar China da ta samo asali, sun hada da Koriya ta kudu inda mutane dubu 6,430 ke dauke da cutar ciki harda sabbi 196, yayin da 42 suka hallaka.

Adadin wadanda ke dauke da cutar a Italiya yakai 3,858, inda tuni 148 suka mutu, kasar Iran wanda ta tabbatar mutuwar mashawarci ga ministan harkokin wajen kasar cikin mutane 124 da suka sheka barzau, yanzu haka mutane 4,747 ne ke dauke da cutar covid-19 a kasar, sai Faransa dake da mutane 423, ciki harda sababbin kamuwa da ita 46, mutanne 9 suka mutu a kasar.

Tuni shugaban kasar Emmanuel Macron ya bukaci Faransawa da su rage ziyarar tsoffi da gajiyyayu da a ganinsa sunfi saurin yada cutar.

Tuni Tsibirin Bhutan, da Kamaru, da yankin Falasdinawa da Serbia, da Fadar Vatican duk suka sanar da bullar cutar a karon farko.

Baya ga tarurruka na addini da siyasa da rufe makarantu da cutar ta haifar, majalisar Turai ta nage zamanta daga Strasbourg zuwa Brussels, yayin da kamfanin shirya fina-finai na kasar India Bollywood dakatar da bikin bada kyaututtuka mafi girma a masana’antar wato "Oscars".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI