Coronavirus: Mutane 110 sun halaka, dubu 3 sun kamu a kwana 1
Wallafawa ranar:
Hukumomin lafiya sun ce zuwa yammacin Jiya Juma’a, jimillar mutane dubu 3 da 456 annobar Coronavirus ta kashe, yayinda wasu dubu 100 da 842 suka kamu da cutar a kasashe da yankuna 92 da annobar ta bulla cikinsu.
Hukumomin lafiyar sun ce cikin kwana daya rak wato daga ranar Alhamis zuwa Juma’a, sai da wannan cuta ta halaka mutane 110, wasu dubu 3 da 332 kuma suka kamu da ita a sassan duniya.
A yanzu haka dai kasashen da annobar ta fi muni cikinsu bayaga China sun hada daKorea ta Kudu, inda annobar ta halaka mutane 42 wasu dubu 6 da 234 suka kamu, sai Italiya inda cutar ta kama mutane dubu 4 da 636 ta kuma halaka wasu 197, sai Iran da annobar ta halakawa mutane 124, wasu dubu 4 da 747 kuma suka kamu. A Faransa kuwa annobar ta Corona ta kashe mutane 9 kawo yanzu, wasu 613 kuma sun kamu.
Jami’an lafiya a China sun ce da safiyar yau asabar kadai karin mutane 28 ne suka halaka a dalilin annobar murar Coronavirus, wadda kawo yanzu ta halaka jimillar mutane dubu 3 da 70 a kasar kadai.
A gefe guda kuma ma’aikatar kididdigar China ta ce kasar ta fuskanci koma baya ta fuskar kayayyakin da take fitarwa zuwa kasuwannin duniya, cikin watannin Janairu da kuma Fabarairu a dalilin annobar Coronavirus, da ta tilasatawa kasashe dakatar da zirga-zirga tsakaninsu.
Binciken ya nuna cewar adadin kayayyakin da China ke fitarwa ya ragu da akalla kashi 17.2 cikin 100, koma baya mafi girma bayan wanda kasar ta gani a lokacin takaddamar kasuwanci tsakaninta daAmurka a farkon 2019.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu