Joe Biden na ci gaba da samun nasara
Wallafawa ranar:
Tsohon Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ya sake samun gagarumar nasara a zaben fidda gwanin Jam’iyyar Democrat da akayi jiya talata a Jihohi 6, abinda ya sa shi a sahun gaba wajen kayar da Sanata Bernie Sanders domin kalubalantar shugaba Donald Trump a zaben watan Nuwamba.
Manazarta na ci gaba da bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden ya lashe jihohi 9 daga cikin jihohi 14 da suka kada kuri’a a zaben Super Tuesday domin fida dan takarar Jam’iyyar Democrat.
Biden ya bada mamaki ganin yadda ya sha gaban babban abokin takararsa, Bernie Sanders a jihar Texas mai muhimmanci.
Sai dai ana hasashen cewa, Mr.Sanders zai yi nasara a California da kuma wasu karin jihohi uku.
‘Yan takarar biyu na kan gaba wajen neman tikitin fafatawa da shugaba Donald Trump a zaben shugaban kasa da za a gudanar a cikin watan Nuwamba mai zuwa.
Tsohon Magajin Garin Birnin New York, Michael Bloomberg ya kashe fiye da rabin Dala biliyan 1 a yakin neman zabensa, amma bai lashe jiha ko daya ba.
Lokacin da yake jawabi jim kadan bayan zaben na daren jiya, Joe Biden ya ce da wadanda suka yi nasara da wadanda aka kayar, dukaninsu wannan yakin neman zabe nasu ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu