Coronavirus

Cutar coronavirus ta shiga kasashen duniya 116

Jami'ai a Koriya ta Kudu suna fesa maganin kashe cutar coronavirus.
Jami'ai a Koriya ta Kudu suna fesa maganin kashe cutar coronavirus. YONHAP / AFP

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka cutar coronavirus ta shiga kasashen duniya 116, inda ta kama mutane 131,460, yayin da ta kashe 4,923.

Talla

Daga ranar Laraba zuwa yau Alhamis, an samu sabbin mutane 7,360 da suka kamu da cutar a kasashe irin su Italiya da Iran da kuma Spain, yayin da 357 suka mutu.

A kasar China kawai an samu mutane 80,793 da suka kamu da cutar tun barkewar ta, wadda ta kashe 3,169 amma banda yankunan ta na Hong Kong da Macau.

A wajen China kuma, mutane 50,668 suka kamu da cutar tun bayan barkewar ta, yayin da ta kashe 1,754.

Kasashen da suka fi fuskantar illar cutar sune China wadda tayi asarar mutane 1,016, sai Italia wadda tayi asarar mutane sana da 1,000 sannan Iran mai mutane 429, sai kuma Spain mai mutane 84.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI