Amurka-Kamaru

Kamaru ta ci zarafin bil'adama- Amurka

Amurka ta zargi mahukunta da kuma jami’an tsaron kasar Kamaru da cin zarafin bil’adama, tare da tsare mutane ba tare da sun aikata wasu laifuka ba.

Shugaban Kamaaru Paul Biya da Mataimakin Sakateren Harkokin Wajen Amurka mai kula da nahiyar Afrika, Tibor Nagy.
Shugaban Kamaaru Paul Biya da Mataimakin Sakateren Harkokin Wajen Amurka mai kula da nahiyar Afrika, Tibor Nagy. Palais_de_lUnité_le_18-03-2019_(c)_PRC_cameroon
Talla

Wadannan zarge-zarge na kunshe ne a cikin rahoton da Amurka ta fitar dangane da batun cin zarafin bil’adama a tsawon shekarar da ta gabata, zargin da a cikinsa Amurka ta ce jami’an tsaron na kashe mutane ba tare da an gurfanar da su gaban kotu ko kuma tabbatar da cewa sun aikata wasu laifuka ba.

Har ila yau rahoton ya yi zargin cewa akwai mutane da dama da suka bace a lokacin da suke tsare a hannun jami’an tsaro, yayin da aka cafke magoya bayan jam’iyyun adawa irun su Maurice Kamto, Penda Ekoka, Paul Eric Kingue duk da cewa daga bisani an sake wasu daga cikinsu.

A wani bangare kuwa, rahoton na Amurka ya yi kakkausar suka a game da yadda mahukuntan Kamaru ke ci gaba da tsare tsohon ministan tsaron cikin gida Marafa Hamidou Yaya wanda aka kama tun 2012 tare da hukuntar da shi saboda rashawa, wannan kuwa da duk da kiran da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kan cewa a sake shi amma har yanzu shiru.

Kasar Kamaru kamar yadda rahoton ya nuna, na da gidajen yari 79 kunshe da fursunoni dubu 23 da 500 kafin karshen 2017, to sai dai a yanzu adadin wadanda ake tsare da su ya kai dubu 30 har da 701.

To amma ko baya ga gwamnatin Paul Biya da kuma jami’an tsaro, rahoton na Amurka ya zargi mayakan ‘yan aware da kuma na Boko Haram da aikata laifufuka a cikin kasar ta Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI