Annobar Coronavirus ta halaka Iraniyawa 97 a kwana 1
Ma’aikatar lafiyar Iran ta ce annobar murar Corona ta halaka karin mutane 97 a yau asabar, abinda ya sanya jimillar adadin wadanda annobar ta halaka a kasar karuwa zuwa 611.
Wallafawa ranar:
A bangaren wadanda suka kamu da cutar kuma, jami’an lafiyar a Iran sun ce karin mutane dubu 1 da 365 aka samu cikin kwana daya rak, abinda ya sanya jimillar adadin wadanda suka kamu kaiwa dubu 12 da 729.
Wasu rahotanni daga kasar ta Iran dai na cewa akalla mutane 92 da suka mutu, sun rasa ransu ne saboda shan sinadarin methanol, bayan da aka shaida musu cewar yana magance cutar murar Coronavirus da ta zamewa duniya annoba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu