Saudiya ta rufe iyakokinta na sama tsawon mako 2 saboda Coronavirus
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Saudiya ta dakatar da saukar jiragen sama cikinta daga kasashe tsawon makwanni 2, domin dakile yaduwar annobar murar coronavirus.
Ma’aikatar harkokin wajen Saudiya ta ce matakin dakatar da zirga-zirgar jiragen saman zai soma aiki ne daga gobe lahadi, wato 15 ga watan Maris da muke ciki.
Sai dai kasar ta ce matakin ba zai shafi wadanda ke da bukata ko kan aiki na musamman ba, kamar abinda ya shafi lafiya ko tsaro.
Yanzu haka dai mutane 86 suka kamu da cutar murar coronavirus a Saudiya sai dai babu hasarar rai, kamar yadda ma’akatar lafiyar kasar ta tabbatar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu