Coronavirus ta tilasta yin hutun karshen mako babu wasanni
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A karon farko an yi hutun karshen mako ba tare da gudanar da gasar wasannin kwararru na kasashen Turai ba, tare da wasu wasanni daban daban da aka shirya yi, saboda yadda cutar coronavirus ta tilasta dakatar da su domin dakile yaduwar ta.
Hukumar kwallon kafar Ingila ta sanar da soke gasar Firimiya har zuwa ranar 5 ga watan gobe.
Tuni aka bayyana cewar mai horar da wasan Arsenal Mikel Arteta da ‘dan wasan Chelsea Callum Hudson-Odoi sun kamu da cutar.
A kasar Italia ‘yan wasa 10 akace sun kamu da cutar, cikin su harda ‘yan wasan kungiyar Fiorentina guda 4 da dan wasan bayan a Juventus.
A Spain an killace ‘yan was an kungiyar Real Madrid abinda ya sa hukumar gasar La Liga dakatar da wasannin na makwanni biyu.
Haka labarin yake a kasashen Faransa da Jamus da Netherlands inda hukumomin kula da wasannin suka bada hutu domin dakile yaduwar cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu