Coronavirus

Turai, Asiya da Gabas ta Tsakiya na ganin takansu

Daya daga cikin yankunan Madrid babban birnin kasar Spain, bayanda annobar coronavirus ta tilasatawa jama'a zaman gida. 15/3/2020.
Daya daga cikin yankunan Madrid babban birnin kasar Spain, bayanda annobar coronavirus ta tilasatawa jama'a zaman gida. 15/3/2020. REUTERS/Sergio Perez

Adadin wadanda annobar murar Coronavirus ke hallakawa na cigaba da karuwa a sassan duniya bayanda kididdigar hukumomin lafiya ta nuna cewar sama da mutane dubu 6 annobar ta halaka.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewar Spain ce kasa ta baya bayan nan da annobar ta yiwa barna, bayan kashe mutane 100, gami da shafarwasu dubu 2 cikin kwana guda.

Tuni dai kasar ta Spain da kuma Faransa suka rufe ilahirin shaguna, gidajen abinci da kasuwanninsu saboda annobar ta coronavirus, bayanda ya tabbata kasashen ke kan gaba wajen fama da cutar murar a nahiyar Turai idan aka dauke Italiya.

A Amurka inda shugaba Donald Trump da yayi gwajin cutar kuma ya tabbata bai kamu ba, ya sanar da fadada haramtawa ‘yan nahiyar Turai shiga kasar zuwa kan Birtaniya da Ireland na tsawon kwanaki 30 saboda wannan annoba.

Iran tace adadin yan kasar da suka mutu dalilin annobar ya kai 724, bayan mutuwarkarin mutane 113 a kwana daya, adadi mafi muni bayan na China, da Italiya.

China kuma inda annobar ta fara bulla, ta bayyana matakin soma killace duk wani dan kasar waje da zarar ya sauka a kasar.

Gwamnatin Austria kuwa ta bada umarnin haramta taron mutane sama da 5, yayinda Norway ta bayyana rufe tashohn jiragen ruwanta ga matafiya daga ketare.

Kasar Kazakhstan shelar kafa dokar ta baci tayi, bayan gano ‘yan kasar 8 da suka kamu da cutar murar ta coronavirus.

A baya bayan nan kuma Jamus tace daga ranar litinin 16 ga watan Maris, za ta rufe iyakokinta da Faransa, Austria da kuma Switzerland saboda annobar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.