Coronavirus ta isa kasashe 142 na duniya, kuma ta kashe 6,501

Adadin Mutanen da cutar coronavirus ta kashe ya tashi zuwa 6,501, yayin da cutar ta kama mutane 168,250 a kasashe 142 na duniya.

Daya daga cikin jami'an tsaron iyakar Iran sanye da mayanin fuska don kariya daga coronavirus.
Daya daga cikin jami'an tsaron iyakar Iran sanye da mayanin fuska don kariya daga coronavirus. REUTERS/Essam al-Sudani
Talla

Alkaluman da hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da kuma wadanda kasashe daban daban suke bayarwa sun nuna cewar kasar Italiya tafi fuskantar illar cutar bayan China, wadda ta kashe mutane 1,860 daga cikin mutane 24,747 da suka kamu.

Iran ta sanar da mutuwar mutane 129 yau litinin abinda ya kawo adadin mutanen da suka mutu a kasar zuwa 853 daga cikin 13,983 da aka tabbatar sun kamu da cutar, sai kuma kasar Spain inda mutane 288 suka mutu daga cikin mutane 7,753 da suka kamu da ita, kana sai Faransa mai mutane 127 da suka mutu daga cikin 5,423 da suka kamu.

Alkaluman da aka tattara yau da safe sun nuna cewar a nahiyar Asia, mutane 92,195 suka kamu da cutar wadda ta kashe 3,337, sai Turai mai mutane 55,176 da suka kamu da ita, yayin da 2,335 suka mutu.

A Gabas ta Tsakiya mutane 15,358 suka kamu da cutar, kuma ta kashe 739, sai Amurka da Canada mai dauke da mutane 4,087 da suka kamu da cutar wadda ta kashe mutane 70.

An tabbatar da cutar a yankin Amurka da kudu da arewa, inda mutane 711 suka kamu, kuma mutane 7 suka mutu, sai Afirka inda mutane 371 suka kamu, kuma 8 suka mutu.

A yankin Oceania mutane 358 suka kamu, kuma mutane 5 sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI