Afghanistan

Coronavirus ta kori mutane dubu 70 daga Iran

Jami'an kiwon lafiya a Iran da ke feshin kashe kwayar cutar Coronavirus a unguwanni
Jami'an kiwon lafiya a Iran da ke feshin kashe kwayar cutar Coronavirus a unguwanni AFP

Hukumomin Afghanistan sun ce, a kalla 'yan kasar 70,000 suka tsere daga Iran a cikin kwanaki 20 domin kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus da ke ci gaba da lakume rayuka.

Talla

Jawed Nadim, shugaban Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ya ce, an bar mutanen sun tsallaka iyaka zuwa cikin kasarsu duk da soke sufurin jiragen sama da kuma zirga-zirgar motoci tsakanin kasahsen biyu.

Jami’in ya ce, suna bukatar karin jami’an kula da lafiya da kuma kayan aiki domin kula da masu dauke da cutar da kuma gwaji ga wadanda suka koma kasar.

Iran ta sanar da mutuwar mutane 853 na ‘yan kasar da suka kamu a sanadiyar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.