Coronavirus

Coronavirus:Bankuna na kokarin bunkasa tattalin arzikin duniya

Coronavirus ta yi rugu-rugu da kasuwannin hannayen jarin kasashen duniya
Coronavirus ta yi rugu-rugu da kasuwannin hannayen jarin kasashen duniya Reuters/路透社

Baitil Malin Amurka da manyan bankunan kasashen duniya sun kaddamar da matakan gaggawa domin farfado da tattalin arzikin duniya da ya shiga mummunan yanayi sakamakon annubar Coronavirus.

Talla

Coronavirus ta dagula al’amura a doran kasa, yayin da gwamnatocin kasashen duniya suka dauki matakan da ba a saba ganin su ba sai a lokutan yaki, da suka hada da matakan rufe kan iyakoki da killace mutane a gida baya ga soke tarukan jama’a.

Ana ci gaba da dari-darin cewa, wannan cuta da ta kassara kusan daukacin bangarori a duniya, za ta haddasa mummunan koma-bayan tattalin azriki, inda kasuwannin hannayen jari ke mummunar faduwa.

Yanzu haka Baitil Malin Amurka ya hubbasa wajen rage fargabar da ake da ita ganin yadda ya dauki tsauraran matakai gabanin bude kasuwannin hannayen jarin Asiya a yau Litinin.

Baitil Malin dai ya zabtare farashin kudin ruwan da yake karba zuwa kusan sifili.

Shi ma babban bankin Japan ya dauki matakin gagagawa na ceto tattalin arzikinsa na uku mafi girma a duniya, kamar yadda manyan bankunan kasashen Turai su ma suka dauki makamancin wannan matakin.

To sai dai a bangare guda, hannayen jarin sun sake girgiza a yau Litinin duk da matakan gaggawar da manyan bankunan duniya suka dauka.

Kazalika kasashen nahiyar Turai da Coronavirus ta fi yi w a illa baya ga China, sun dakatar da al’amura da dama a farkon wannan mako, yayin da manyan biranen Amurka suka rufe gidajen sharholiya da kuma wuraren cin abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.